Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 21:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan haka Yesu ya sāke bayyana kansa ga almajiran a bakin Tekun Tibariya. Ga kuwa yadda ya bayyana kansa.

2. Bitrus, da Toma wanda ake kira Ɗan Tagwai, da Nata'ala na Kana ta ƙasar Galili, da 'ya'yan nan na Zabadi, da kuma waɗansu almajiransa biyu, duk suna nan tare,

3. Sai Bitrus ya ce musu, “Za ni su.” Suka ce masa, “Mu ma mā tafi tare da kai.” Sai suka fita suka shiga jirgi. Amma a daren nan ba su kama kome ba.

4. Gari na wayewa sai ga Yesu tsaye a bakin gaci, amma almajiran ba su gane Yesu ne ba.

5. Sai Yesu ya ce musu, “Samari, kuna da kifi?” Suka amsa masa suka ce, “A'a.”

Karanta cikakken babi Yah 21