Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 20:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, a ranar farko ta mako, Maryamu Magadaliya ta je kabarin da asuba, tun da sauran duhu, ta ga an kawar da dutsen daga kabarin.

2. Sai ta yiwo gudu wurin Bitrus da kuma almajirin nan da Yesu yake ƙauna, ta ce musu, “An ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuwa san inda aka sa shi ba.”

3. Sai Bitrus da almajirin nan suka fita suka doshi kabarin.

4. Duka biyu suka ruga a guje, amma almajirin nan ya tsere wa Bitrus, ya riga isa kabarin.

5. Yana duƙawa yana leƙa ciki, sai ya ga likkafanin lilin a ajiye, amma fa bai shiga ba.

6. Sa'an nan Bitrus ya zo a bayansa, ya kuwa shiga kabarin, ya ga likkafanin a ajiye,

7. mayanin kuma da yake kansa ba a ajiye tare da likkafanin yake ba, amma a naɗe shi kaɗai a waje ɗaya.

8. Sai almajirin nan da ya riga isa kabarin shi ma ya shiga, ya gani, ya kuma ba da gaskiya.

9. Don kafin lokacin nan ba su fahimci Nassin nan ba, cewa lalle ne yă tashi daga matattu.

Karanta cikakken babi Yah 20