Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 18:19-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. Sai babban firist ya tuhumi Yesu a kan almajiransa da kuma koyarwa tasa.

20. Yesu ya amsa masa ya ce, “Ai, na yi wa duniya magana a bayyane, na kuma sha koyarwa a majami'u da Haikali inda Yahudawa duka sukan taru. Ban faɗi kome a ɓoye ba.

21. Don me kake tuhumata? Tuhumi waɗanda suka saurare ni a kan abin da na faɗa musu, ai, sun san abin da na faɗa.”

22. Da ya faɗi haka, wani daga cikin dogaran da suke tsaye kusa, ya mari Yesu, ya ce, “Haka za ka amsa wa babban firist?”

23. Yesu ya amsa masa ya ce, “In na faɗi mugun abu to, ka ba da shaida kan haka. In kuwa daidai na faɗa, to, don me za ka mare ni?”

24. Sai Hanana ya aika da shi a ɗaure wurin Kayafa, babban firist.

25. To, Bitrus kuwa yana tsaye yana jin wuta. Sai suka ce masa, “Anya! Kai ma ba cikin almajiransa kake ba?” Sai ya mūsu ya ce, “A'a, ba na ciki.”

26. Sai wani daga cikin bayin babban firist, wato dangin wanda Bitrus ya fille wa kunne, ya ce, “Ashe, ban gan ka tare da shi a lambun ba?”

27. Sai Bitrus ya sāke yin musu. Nan da nan kuwa zakara ya yi cara.

28. Daga wurin Kayafa kuma suka kai Yesu fādar mai mulki. Da asuba ne kuwa. Su kansu ba su shiga fādar ba, wai don kada su ƙazantu su kāsa cin jibin Ƙetarewa.

29. Saboda haka, Bilatus ya fito wajensu, ya ce, “Wace ƙara kuka kawo ta mutumin nan?”

30. Sai suka amsa masa suka ce, “Da wannan ba mai laifi ba ne, ai, da ba mu bāshe shi gare ka ba.”

31. Bilatus ya ce musu, “Ku tafi da shi da kanku mana, ku hukunta shi bisa ga shari'arku!” Sai Yahudawa suka ce masa, “Ai, ba mu da ikon zartar da hukuncin kisa a kan kowa.”

32. Wannan kuwa don a cika maganar da Yesu ya yi ne, wadda ta kwatanta irin mutuwar da zai yi.

33. Sai Bilatus ya koma cikin fāda, ya kira Yesu ya ce masa, “Ashe, kai ɗin nan, kai ne Sarkin Yahudawa?”

34. Yesu ya amsa ya ce, “Wato wannan faɗarka ce, ko kuwa waɗansu ne suka ce da ni haka a wurinka?”

Karanta cikakken babi Yah 18