Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 18:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan Yesu ya yi maganan nan, ya fita, shi da almajiransa zuwa hayin Rafin Kidron, inda wani lambu yake, ya kuma shiga da almajiransa.

2. Yahuza ma wanda ya bāshe shi ya san wurin, domin Yesu ya saba haɗuwa da almajiransa a can.

3. Yahuza kuwa bayan ya ɗauko ƙungiyar soja, da waɗansu dogaran Haikali daga manyan firistoci da Farisiyawa, suka zo wurin, riƙe da fitilu, da jiniyoyi, da makamai,

4. Yesu kuwa da ya san duk abin da zai same shi, ya yiwo gaba, ya ce musu, “Wa kuke nema?”

5. Suka amsa masa suka ce, “Yesu Banazare.” Yesu ya ce musu, “Ni ne.” Yahuza kuwa da ya bāshe shi yana tsaye tare da su.

6. Da Yesu ya ce musu, “Ni ne,” suka ja da baya da baya, har suka fāɗi.

7. Sai ya sāke tambayarsu, “Wa kuke nema?” Suka ce, “Yesu Banazare.”

8. Yesu ya amsa ya ce, “Ai, na gaya muku, ni ne. In kuwa ni kuke nema, ku bar waɗannan su tafi.”

9. Wannan kuwa domin a cika maganar da ya yi ne cewa, “A cikin waɗanda ka ba ni ban yar da ko ɗaya ba.”

Karanta cikakken babi Yah 18