Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 17:18-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Kamar yadda ka aiko ni duniya, haka ni ma na aike su duniya.

19. Saboda su ne nake miƙa kaina, domin su ma a tsarkake su cikin gaskiya.

20. “Ba kuwa waɗannan kaɗai nake roƙa wa ba, har ma masu gaskatawa da ni ta maganarsu,

21. domin dukansu su zama ɗaya, kamar yadda kai, ya Uba, kake cikina, ni kuma nake cikinka, haka su ma su kasance cikinmu, domin duniya ta gaskata, cewa kai ne ka aiko ni.

22. Ɗaukakar da ka yi mini, ita na yi musu, domin su zama ɗaya kamar yadda muke ɗaya,

23. ni a cikinsu, kai kuma a cikina, domin su zama ɗaya sosai, duniya ta gane kai ne ka aiko ni, ta kuma gane ka ƙaunace su kamar yadda ka kaunace ni.

24. Ya Uba, ina so waɗanda ka ba ni, su ma su kasance tare da ni inda nake, su dubi ɗaukakata da ka yi mini, domin ka ƙaunace ni tun ba a halicci duniya ba.

25. Ya Uba mai adalci, duniya kam, ba ta san ka ba, amma ni na san ka , waɗannan kuma sun sani kai ne ka aiko ni.

26. Na sanar da su sunanka, zan kuma sana, domin ƙaunar da ka yi mini tă kasance cikinsu, ni ma in kasance a cikinsu.”

Karanta cikakken babi Yah 17