Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 15:1-7 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ni ne itacen inabi na hakika, Ubana kuwa shi ne manomi.

2. Kowane reshe a cikina da ba ya 'ya'ya, sai ya datse shi. Kowane reshe mai yin 'ya'ya kuwa yakan tsarkake shi don ya ƙara haihuwa.

3. Koyanzu ma ku tsarkakku ne saboda maganar da na faɗa muku.

4. Ku zauna a cikina, ni kuma a cikinku. Kamar yadda reshen inabi, ba ya iya 'ya'ya shi kaɗai, sai ko ya zauna itacen inabin, haka ku ma ba za ku iya ba, sai kun zauna a cikina.

5. Ni ne itacen inabin, ku kuwa rassan. Wanda ya zauna a cikina, ni kuma a cikinsa, shi ne mai yin 'ya'ya da yawa. Domin in ba game da ni ba, ba za ku iya kome ba.

6. Duk wanda bai zauna a cikina ba, za a yar da shi can, kamar reshe, yă bushe, a kuma tattara irinsu a jefa wuta, a ƙone.

7. In kun zauna a cikina, maganata kuma ta zauna a cikinku, za ku roƙi duk abin da kuke so, za a kuwa yi muku.

Karanta cikakken babi Yah 15