Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 12:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Da taron Yahudawa mai yawa suka ji labari yana nan, sai suka zo, ba domin Yesu kaɗai ba, har ma don su ga Li'azaru wanda ya tasa daga matattu.

10. Sai manyan firistoci suka yi shawarar kashe Li'azaru, shi ma,

11. domin ta dalilinsa Yahudawa da yawa suke warewa, suna gaskatawa da Yesu.

12. Kashegari babban taron da suka zo idi, da suka ji Yesu yana zuwa Urushalima,

13. suka ɗaɗɗauko gazarin dabino suka firfita taryensa, suna ta da murya suna cewa, “Hosanna! Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji, Sarkin Isra'ila!”

14. Da Yesu ya sami wani jaki sai ya hau, yadda yake a rubuce cewa,

15. “Kada ki ji tsoro, ya ke 'yar Sihiyona,Ga sarkinki na zuwa a kan aholakin jaki!”

16. Da fari almajiransa ba su gane abin nan ba, amma bayan an ɗaukaka Yesu, suka tuna abin nan a rubuce yake game da shi, har ma aka yi masa shi.

17. Taron da yake tare da shi sa'ad da ya kira Li'azaru yă fito daga kabari, ya tashe shi daga matattu, su suka riƙa shaidarwa da haka.

18. Shi ya sa taron suka fita taryensa, don sun ji ya yi mu'ujizan nan.

19. Sai Farisiyawa suka ce wa juna, “Kun ga! Ba abin da muka iya! Ai, duk duniya tana bayansa.”

Karanta cikakken babi Yah 12