Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 12:37-50 Littafi Mai Tsarki (HAU)

37. Amma ko da yake ya sha yin mu'ujizai da yawa a gabansu, duk da haka, ba su gaskata shi ba,

38. domin a cika faɗar Annabi Ishaya cewa,“Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?Ga wa kuma aka bayyana ikon Ubangiji?”

39. Shi ya sa ba su iya ba da gaskiya ba. Domin Ishaya ya sāke cewa,

40. “Ya makantar da su, ya kuma taurarar da zuciya tasu,Kada su gani da idanunsu, su kuma gane a zuci,Har su juyo gare ni in warkar da su.”

41. Ishaya ya faɗi haka saboda ya ga ɗaukakar Almasihu, ya kuma ba da labarinsa.

42. Duk da haka, da yawa har daga cikin shugabanni ma suka gaskata da shi, amma saboda tsoron Farisiyawa, ba su bayyana ba, don kada a fisshe su daga jama'a.

43. Don sun fi ƙaunar girmamawar mutane da girmamawar Allah.

44. Sai Yesu ya ɗaga murya ya ce, “Wanda yake gaskatawa da ni, ba da ni yake gaskatawa ba, amma ga wanda ya aiko ni ne.

45. Wanda kuma yake dubana, yana duban wanda ya aiko ni ne.

46. Na zo duniya a kan ni haske ne, domin duk mai gaskatawa da ni kada ya yi zaman duhu.

47. Kowa ya ji maganata, bai kuwa kiyaye ta ba, ba ni nake hukunta shi ba. Gama ba don yi wa duniya hukunci na zo ba, sai dai domin in ceci duniya.

48. Wanda ya ƙi ni, bai kuma karɓi maganata ba, yana da mai hukunta shi, maganar da na faɗa, ita za ta hukunta shi a ranar ƙarshe.

49. Ba kuwa domin kaina na yi magana ba, Uban da ya aiko ni shi kansa ya ba ni umarni a kan abin da zan faɗa, da kuma maganar da zan yi.

50. Na kuma san umarnin nan nasa rai ne madawwami. Domin haka, abin da nake faɗa ina faɗa ne daidai yadda Uba ya faɗa mini.”

Karanta cikakken babi Yah 12