Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 11:7-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.”

8. Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?”

9. Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan.

10. Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!”

11. Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”

12. Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.”

13. Alhali kuwa, Yesu zancen mutuwar Li'azaru yake, amma su sun ɗauka yana nufin barcin hutawa ne.

14. Sai Yesu ya gaya musu a fili, ya ce, “Li'azaru dai ya mutu.

15. Ina kuwa farin ciki da ba na nan, saboda ku domin ku ba da gaskiya. Amma mu dai je wurinsa.”

16. Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”

17. Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari.

18. Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu.

19. Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu.

20. Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida.

21. Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba.

22. Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.”

23. Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.”

Karanta cikakken babi Yah 11