Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 11:29-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa.

30. Yesu dai bai iso ƙauyen ba tukuna, har yanzu yana wurin da Marta ta tarye shi.

31. Da Yahudawan da suke tare da ita a cikin gida, suna yi mata ta'aziyya, suka ga Maryamu ta yi maza ta tashi ta fita, suka bi ta, suna zaton za ta kabarin ne, ta yi kuka a can.

32. Da Maryamu ta iso inda Yesu yake, ta gan shi, sai ta faɗi a gabansa ta ce masa, “Ya Ubangiji, da kana nan da dan'uwana bai mutu ba.”

33. Da Yesu ya ga tana kuka, Yahudawan da suka zo tare da ita su ma, suna kuka, sai ya nisa a ransa, ya yi juyayi gaya.

34. Ya kuma ce, “Ina kuka sa shi?” Suka ce masa, “Ya Ubangiji, zo ka gani.”

35. Sai Yesu ya yi hawaye.

36. Don haka Yahudawa suka ce, “Dubi yadda yake ƙaunarsa!”

37. Amma waɗansunsu suka ce, “Ashe, wanda ya buɗe wa makahon nan ido, ba zai iya hana wannan mutum mutuwa ba?”

Karanta cikakken babi Yah 11