Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 11:16-29 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Sai Toma, wanda ake kira Ɗan Tagwai, ya ce wa 'yan'uwansa almajirai, “Mu ma mu tafi, mu mutu tare da shi.”

17. Da Yesu ya isa, ya tarar Li'azaru, har ya kwana huɗu a kabari.

18. Betanya kuwa kusa da Urushalima take, misalin mil biyu.

19. Yahudawa da yawa sun zo su yi wa Marta da Maryamu ta'aziyyar ɗan'uwansu.

20. Da jin Yesu na zuwa, sai Marta ta je taryensa, Maryamu kuwa ta zauna a gida.

21. Sai Marta ta ce wa Yesu, “Ya Ubangiji, da kana nan da ɗan'uwana bai mutu ba.

22. Ko yanzu ma na sani kome ka roƙi Allah zai yi maka.”

23. Yesu ya ce mata, “Ɗan'uwanki zai tashi.”

24. Marta ta ce masa, “Na sani zai tashi a tashin matattu a ranar ƙarshe.”

25. Yesu ya ce mata, “Ai, ni ne tashin matattu, ni ne kuma rai. Wanda ya gaskata da ni, ko ya mutu zai rayu.

26. Wanda kuwa yake raye, yake kuma gaskatawa da ni, ba zai mutu ba har abada. Kin gaskata wannan?”

27. Ta ce masa, “I, ya Ubangiji. Na gaskata kai ne Almasihu, Ɗan Allah, shi wannan mai zuwa duniya.”

28. Da ta faɗi haka, ta je ta kirawo 'yar'uwa tata Maryamu, ta raɗa mata ta ce, “Ga Malam ya zo, yana kiranki.”

29. Ita kuwa da jin haka, ta yi maza ta tashi ta nufi wurinsa.

Karanta cikakken babi Yah 11