Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 11:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wani mutum ne ya yi rashin lafiya, sunansa Li'azaru na Betanya, ƙauyen su Maryamu da 'yar'uwarta Marta.

2. Maryamun nan kuwa, wadda ɗan'uwanta Li'azaru ba shi da lafiya, ita ce wadda ta shafa wa Ubangiji man ƙanshi, ta kuma shafe ƙafafunsa da gashinta.

3. To, 'yan'uwan nan mata suka aika masa, suka ce, “Ya Ubangiji, ga shi, wanda kake ƙaunan nan ba shi da lafiya.”

4. Da Yesu ya ji haka ya ce, “Wannan rashin lafiya, ƙarshensa ba mutuwa ba ne, domin a ɗaukaka Allah ne, a kuma ɗaukaka Ɗan Allah ta wurinsa.”

5. Yesu kuwa na ƙaunar Marta da 'yar'uwarta, da kuma Li'azaru.

6. To, da ya ji Li'azaru ba shi da lafiya, sai ya ƙara kwana biyu.

7. Bayan haka ya ce wa almajiran, “Mu koma ƙasar Yahudiya.”

8. Almajiran suka ce masa, “Ya Shugaba, kwana kwanan nan fa Yahudawa suke neman jifanka, za ka sāke komawa can?”

9. Yesu ya amsa ya ce, “Ba sa'a goma sha biyu ce yini ɗaya ba? Kowa yake tafiya da rana ba ya tuntuɓe, don yana ganin hasken duniyan nan.

10. Amma kowa yake tafiya da dare yakan yi tuntuɓe, don ba haske a gare shi!”

11. Ya faɗi haka, sa'an nan ya ƙara ce musu, “Amininmu Li'azaru ya yi barci, amma za ni in tashe shi.”

12. Sai almajiran suka ce masa, “Ya Ubangiji, in dai barci ne ya ɗauke shi, ai, zai warke.”

Karanta cikakken babi Yah 11