Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 10:11-28 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ni ne makiyayi mai kyau. Makiyayi mai kyau kuwa shi ne mai ba da ransa domin tumakin.

12. Wanda yake ɗan asako kuwa, ba makiyayin gaske ba, tumakin kuma ba nasa ba, da ganin kyarkeci ya doso, sai ya watsar da tumakin, ya yi ta kansa, kyarkeci kuwa ya sure waɗansu, ya fasa sauran.

13. Ya gudu ne fa, don shi ɗan asako ne, ba abin da ya dame shi da tumakin.

14. Ni ne Makiyayi mai kyau. Na san nawa, nawa kuma sun san ni,

15. kamar yadda Uba ya san ni, ni kuma na san Uban. Ina ba da raina maimakon tumakin.

16. Ina kuma da waɗansu tumaki da ba na wannan garke ba ne. Su ma lalle in kawo su, za su kuwa saurari muryata, su zama garke guda, makiyayi kuma guda.

17. Domin wannan uba yake ƙaunata, domin ina ba da raina in ɗauko shi kuma.

18. Ba mai karɓe mini rai, don kaina nake ba da shi. Ina da ikon ba da shi, ina da ikon ɗauko shi kuma. Na karɓo wannan umarni ne daga wurin Ubana.”

19. Saboda maganan nan fa, sai rabuwa ta sāke shiga tsakanin Yahudawa.

20. Da yawa daga cikinsu suka ce, “Ai, mai iska ne, haukansa kawai yake yi. Don me za ku saurare shi?”

21. Waɗansu kuwa suka ce, “A'a, wannan magana, ai, ba ta mai iska ba ce. Ashe, iska tana iya buɗe wa makaho ido?”

22. Lokacin idin tsarkakewa ne kuwa a Urushalima,

23. damuna ce kuma, Yesu kuwa na zagawa a Shirayin Sulemanu cikin Haikali,

24. sai Yahudawa suka kewaye shi, suka ce masa, “Har yaushe za ka bar mu da shakka? In dai kai ne Almasihun, ka gaya mana a fili.”

25. Yesu ya amsa musu ya ce, “Ai, na faɗa muku, ba ku gaskata ba. Ayyukan da nake yi da sunan Ubana, suke shaidata.

26. Amma ku ba ku gaskata ba, domin ba kwa cikin tumakina.

27. Tumakin nan nawa sukan saurari muryata, na san su, suna kuma bi na.

28. Ina ba su rai madawwami, ba kuwa za su halaka ba har abada, ba kuma mai ƙwace su daga hannuna.

Karanta cikakken babi Yah 10