Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 10:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Lalle hakika, ina gaya muku, wanda bai shiga garken tumaki ta ƙofa ba, amma ya haura ta wani gu, to, shi ɓarawo ne, ɗan fashi kuma.

2. Wanda kuwa ya shiga ta ƙofar, makiyayin tumakin ne.

3. Mai tsaron ƙofar yakan buɗe masa, tumakin kuma sukan saurari murya tasa, yakan kama sunan nasa tumaki, ya kai su waje.

4. Bayan ya fitar da dukan nasa waje, sai ya shige gabansu, tumakin na biye da shi, domin sun san murya tasa.

5. Ba za su bi baƙo ba, sai dai su guje shi, don ba su san muryar baƙo ba.”

6. Yesu ya yi musu wannan misali, amma ba su gane abin da ya faɗa musu ba.

7. Don haka Yesu ya sāke ce musu, “Lalle hakika, ina gaya muku, ni ne ƙofar tumakin.

8. Duk waɗanda suka riga ni zuwa cewa, su ne ni, ɓarayi ne, 'yan fashi kuma, amma tumakin ba su kula da su ba.

9. Ni ne ƙofar. Kowa ya shiga ta wurina zai sami ceto, ya kai ya kawo, ya kuma yi kiwo.

Karanta cikakken babi Yah 10