Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 1:17-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance.

18. Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

19. Wannan kuwa ita ce shaidar Yahaya, wato, sa'ad da Yahudawa suka aiki firistoci da Lawiyawa daga Urushalima su tambaye shi, ko shi wane ne.

20. Sai ya faɗi gaskiya, bai yi musu ba, gaskiya ya faɗa ya ce, “Ba ni ne Almasihu ba.”

21. Sai suka tambaye shi, “To, yaya, Iliya ne kai?” Ya ce, “A'a, ba shi ba ne.” Suka ce, “Kai ne annabin nan?” Ya ce, “A'a.”

22. Sai suka ce masa, “To, wane ne kai, domin mu sami amsar da za mu mayar wa waɗanda suka aiko mu? Me kake ce da kanka?”

23. Ya ce, “Ni murya ce ta mai kira a jeji, mai cewa, ‘Ku miƙe wa Ubangiji tafarki,’ yadda Annabi Ishaya ya faɗa.”

24. Su kuwa, Farisiyawa ne suka aiko su.

25. Sai suka tambaye shi suka ce, “To, don me kake yin baftisma in kai ba Almasihu ba ne, ba kuwa Iliya ba, ba kuma annabin nan ba?”

26. Sai Yahaya ya amsa musu ya ce, “Ni kam, da ruwa nake baftisma, amma da wani nan tsaye a cikinku wanda ba ku sani ba,

27. shi ne mai zuwa bayana, wanda ko maɓallin takalminsa ma, ban isa in ɓalle ba.”

28. An yi wannan a Betanya ne, a hayin Kogin Urdun, inda Yahaya yake yin baftisma.

29. Kashegari Yahaya ya tsinkayo Yesu na nufo shi, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah, wanda zai ɗauke zunubin duniya!

30. Wannan shi ne wanda na ce, ‘Wani yana zuwa bayana, wanda ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’

31. Dā kam, ban san shi ba, sai domin a bayyana shi ga Isra'ila na zo, nake baftisma da ruwa.”

32. Yahaya ya yi shaida ya ce, “Na ga Ruhu na saukowa kamar kurciya daga sama, ya kuma zauna a kansa.

33. Dā kam, ban san shi ba, sai dai wanda ya aiko ni in yi baftisma da ruwa, shi ne ya ce mini, ‘Wanda ka ga Ruhun na sauko masa, yana kuma kasance a kansa, shi ne mai yin baftisma da Ruhu Mai Tsarki.’

34. Na kuwa gani, na kuma yi shaida, cewa wannan Ɗan Allah ne.”

35. Kashegari kuma Yahaya na tsaye da almajiransa biyu.

36. Yana duban Yesu na tafiya, sai ya ce, “Kun ga, ga Ɗan Rago na Allah!”

37. Almajiran nan biyu suka ji ya faɗi haka, sai suka bi Yesu.

Karanta cikakken babi Yah 1