Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Yah 1:1-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne.

2. Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah.

3. Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi.

4. Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane.

5. Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.

6. Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya.

7. Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa.

8. Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.

9. Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum.

10. Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba.

Karanta cikakken babi Yah 1