Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 9:13-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sa'an nan mala'ika na shida ya busa ƙahonsa, sai na ji wata murya daga zankayen nan huɗu na bagadin ƙona turare na zinariya a gaban Allah,

14. tana ce wa mala'ikan nan na shida mai ƙaho, “Ka saki mala'iku huɗun nan da suke a ɗaure a gabar babban kogin nan Yufiretis.”

15. Sai aka saki mala'ikun nan huɗu, waɗanda aka tanada saboda wannan sa'a, da wannan rana, da wannan wata, da wannan shekara, su kashe sulusin 'yan adam.

16. Yawan rundunonin sojan doki kuwa, na ji adadinsu zambar dubu metan ne.

17. Ga kuwa yadda na ga dawakan a wahayin da aka yi mini, mahayansu suna saye da sulkuna, launinsu ja kamar wuta, da shuɗi, da kuma rawaya kamar farar wuta, kawunan dawakan kuma kamar na zaki, wuta kuma da hayaƙi da farar wuta suna fita daga bakinsu.

18. Da waɗannan bala'i uku aka kashe sulusin 'yan adam, wato, da wuta, da hayaƙi, da farar wuta da suke fita daga bakinsu.

Karanta cikakken babi W. Yah 9