Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 8:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da Ɗan Ragon ya ɓamɓare hatimi na bakwai, aka yi shiru a Sama kamar na rabin sa'a.

2. Sa'an nan na ga mala'ikun nan bakwai da suke a tsaye a gaban Allah, an ba su ƙaho bakwai.

3. Ga kuma wani mala'ika ya zo ya tsaya a gaban bagadin ƙona turare, riƙe da tasar zinariya ta turaren ƙonawa. Sai aka ba shi turare mai yawa, domin ya haɗa da addu'o'in tsarkaka duka a kan bagadin ƙona turare na zinariya a gaban kursiyin.

4. Sai hayaƙin turaren ya tashi daga hannun mala'ikan tare da addu'o'in tsarkaka, ya isa a gaban Allah.

5. Sai mala'ikan ya ɗauki tasar nan ta turaren ƙonawa, ya cika ta da wuta daga bagadin ƙona turare, ya watsa a kan duniya, sai aka yi ta aradu, da ƙararraki masu tsanani, da walƙiya, da kuma rawar ƙasa.

6. Sa'an nan mala'ikun nan bakwai masu ƙaho bakwai ɗin nan, suka yi shirin busa su.

7. Mala'ikan farko ya busa ƙahonsa, sai ga ƙanƙara da wuta, gauraye da jini. Aka zuba su a duniya, sai sulusin duniya ya ƙone, sulusin itatuwa suka ƙone, dukkan ɗanyar ciyawa kuma ta ƙone.

8. Mala'ika na biyu ya busa ƙahonsa, sai aka jefa wani abu a teku kamar babban dutse mai tsawo, mai cin wuta. Sulusin teku ya zama jini,

9. sulusin halittar da suke a ruwa suka mutu, sulusin jiragen ruwa kuma suka hallaka.

Karanta cikakken babi W. Yah 8