Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 7:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. dubu goma sha biyu daga kabilar Saminu, dubu goma sha biyu daga kabilar Lawi, dubu goma sha biyu daga kabilar Issaka,

8. dubu goma sha biyu daga kabilar Zabaluna, dubu goma sha biyu daga kabilar Yusufu, dubu goma sha biyu kuma daga kabilar Biliyaminu.

9. Bayan wannan na duba, ga wani ƙasaitaccen taro, wanda ya fi gaban ƙirge, daga kowace al'umma, da kabila, da jama'a, da harshe, suna a tsaitsaye a gaban kursiyin, a gaban Ɗan Ragon kuma, a saye da fararen riguna, da gazarin dabino a hannunsu,

10. suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”

11. Dukan mala'iku kuwa suna tsaitsaye a kewaye da kursiyin, da dattawan nan, da kuma rayayyun halittan nan guda huɗu, suka fāɗi a gaban kursiyin suka yi wa Allah sujada,

12. suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahnmu har abada abadin! Amin! Amin!”

13. Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Su wane ne waɗannan da suke a saye da fararen riguna, daga ina kuma suke?”

14. Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.

Karanta cikakken babi W. Yah 7