Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 7:12-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

12. suna cewa, “Hakika! Yabo, da ɗaukaka, da hikima, da godiya, da girma, da iko, da ƙarfi su tabbata ga Allahnmu har abada abadin! Amin! Amin!”

13. Sai ɗaya daga cikin dattawan nan ya yi mini magana, ya ce, “Su wane ne waɗannan da suke a saye da fararen riguna, daga ina kuma suke?”

14. Sai na ce masa, “Ya shugaba, ai, ka sani.” Sai ya ce mini, “Su ne waɗanda suka fito daga matsananciyar wahala, sun wanke rigunansu, suka mai da su farare da jinin Ɗan Ragon nan.

15. Saboda haka ne suke a gaban kursiyin Allah, suna bauta masa dare da rana a Haikalinsa. Na zaune a kan kursiyin nan kuwa, zai kare su da Zatinsa,

16. ba za su ƙara jin yunwa ba, ba kuma za su ƙara jin ƙishirwa ba, ba za su ƙara jin zafin rana ko ƙuna ba sam,

17. domin Ɗan Ragon nan da yake a tsakiyar kursiyin, shi zai zama makiyayinsu, zai kuwa kai su maɓuɓɓugar ruwan rai. Allah kuma zai share musu dukan hawaye.”

Karanta cikakken babi W. Yah 7