Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 6:13-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. taurari kuma suka faɗa a ƙasa kamar yadda ɓaure yake zubar da ɗanyun 'ya'yansa, in ƙasaitacciyar iska ta kaɗa shi,

14. sararin sama ya dāre ya naɗe kamar tabarma, sai aka kawar da kowane dutse, da kowane tsibiri daga mazauninsa.

15. Sai sarakunan duniya, da manyan mutane, da sarakunan yaƙi, da ma'arzuta, da ƙarfafa, da kuma kowane bawa da ɗa, suka ɓuya a kogwanni, da kuma a cikin duwatsu,

16. suna ce wa duwatsun, “Ku faɗo a kanmu, ku ɓoye mu daga idon wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma fushin Ɗan Ragon nan,

17. don babbar ranar fushinsu ta zo, wa kuwa zai iya jure mata?”

Karanta cikakken babi W. Yah 6