Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 3:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Sardisu haka, ‘Ga maganar mai Ruhohin Allah guda bakwai, da kuma taurarin nan bakwai.“ ‘Na san ayyukanka, kai rayayye ne, alhali kuwa matacce ne kai.

2. Ka yi zaman tsaro, ka ƙarfafa abin nan da ya saura, yake kuma a bakin mutuwa, don ban ga aikinka cikakke ne ba a gaban Allahna.

3. Don haka, sai ka tuna da abin da ka karɓa ka kuma ji, ka kiyaye shi, sa'an nan ka tuba. In ba za ka yi tsaro ba, zan zo kamar ɓarawo, ba kuwa za ka san a lokacin da zan auko maka ba.

4. Amma dai har yanzu kana da waɗansu kaɗan a Sardisu da ba su ƙazantar da kansu ba, za su kuwa kasance tare da ni da fararen kaya, don sun cancanta.

5. Duk wanda ya ci nasara, za a sa masa fararen tufafi, ba kuwa zan soke sunansa daga Littafin Rai ba, zan ce shi nawa ne a gaban Ubana, da kuma a gaban mala'ikunsa.

6. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikilisiyoyi.’ ”

7. “Ka kuma rubuta wa mala'ikan ikkilisiyar da take a Filadalfiya haka, ‘Ga maganar Mai Tsarkin nan, Mai gaskiya, wanda yake da mabuɗin Dawuda, wanda in ya buɗe, ba mai rufewa, in kuma ya rufe, ba mai buɗewa.

8. “ ‘Na san ayyukanka. Ka ga, na bar maka ƙofa a buɗe, wadda ba mai iya rufewa. Na dai san ƙarfinka kaɗan ne, duk da haka, kā kiyaye maganata, ba ka yi musun sanin sunana ba.

9. To, ga shi, zan sa su waɗanda suke daga jama'ar Shaiɗan, masu cewa su Yahudawa ne, alhali kuwa ba su ba ne, ƙarya suke yi, zan sa su, su zo, su kwanta a gabanka, su sani dai na ƙaunace ka.

Karanta cikakken babi W. Yah 3