Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 21:9-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sai kuma ɗaya daga cikin mala'ikun nan bakwai, masu tasoshin nan bakwai, cike da bala'i bakwai na ƙarshe, ya zo ya yi mini magana, ya ce, “Zo in nuna maka amarya, matar Ɗan Ragon.”

10. Sai ya ɗauke ni, Ruhu yana iza ni, ya kai ni wani babban dutse mai tsawo, ya nuna mini tsattsarkan birnin Urushalima yana saukowa daga Sama daga wurin Allah,

11. yana tare da ɗaukakar Allah. Hasken birnin yana ƙyalƙyali kamar wani irin nadirin dutse mai daraja, kamar yasfa, garau kamar ƙarau.

12. Yana da babban garu mai tsawo, da ƙofar gari goma sha biyu, a ƙofofi ɗin da akwai mala'iku goma sha biyu. A jikin ƙofofin kuma an rubuta sunayen kabilan nan goma sha biyu na Isra'ila,

13. a gabas, ƙofa uku, a yamma ƙofa uku, a kudu ƙofa uku, a arewa kuma ƙofa uku.

14. Garun birnin kuwa, tana da dutsen harsashi goma sha biyu, a jikinsu kuma an rubuta sunayen manzannin nan goma sha biyu na Ɗan Ragon.

15. Shi wanda ya yi mini magana kuwa yana da sandar awo ta zinariya, domin ya auna birnin, da ƙofofinsa, da garunsa.

Karanta cikakken babi W. Yah 21