Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 21:19-27 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. An kuma ƙawata harsasan garun birnin da kowane irin dutse mai daraja. Yasfa shi ne na farko, na biyu saffir, na uku agat, na huɗu zumurrudu,

20. na biyar onis, na shida yaƙutu, na bakwai kirisolat, na takwas beril, na tara tofaz, na goma kirisofaras, na sha ɗaya yakinta, na sha biyu kuma ametis.

21. Ƙofofin gari goma sha biyun nan kuwa lu'ulu'u ne goma sha biyun, kowace ƙofa da lu'ulu'u guda aka yi ta, hanyar birnin kuwa zinariya ce zalla garau kamar ƙarau.

22. Ban kuwa ga wani Haikali a birnin ba, domin Haikalinsa Ubangiji Allah Maɗaukaki ne, da kuma Ɗan Ragon.

23. Birnin kuwa ba ya bukatar rana ko wata su haskaka shi, domin ɗaukakar Allah ita ce haskensa, Ɗan Ragon kuma fitilarsa.

24. Da haskensa al'ummai za su yi tafiya. Sarakunan duniya za su kawo darajarsu a gare shi.

25. Ƙofofinsa kuwa ba za a rufe su da rana ba har abada, ba kuwa za a yi dare a can ba.

26. Za a kuma kawo darajar al'ummai da girmansu a gare shi.

27. Amma ko kaɗan ba wani abu marar tsarki da zai shiga cikinsa, ko wani mai aikata abin ƙyama ko ƙarya, sai dai waɗanda aka rubuta sunayensu a Littafin Rai na Ɗan Ragon kaɗai.

Karanta cikakken babi W. Yah 21