Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 20:1-5 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'an nan na ga wani mala'ika yana saukowa daga Sama, yana a riƙe da mabuɗin mahallaka, da kuma wata babbar sarƙa a hannunsa.

2. Sai ya kama macijin nan, wato, macijin nan na tun dā dā, wanda yake shi ne Ibilis, shi ne kuma Shaiɗan, ya ɗaure shi har shekara dubu,

3. ya jefa shi mahallakar, ya rufe, ya kuma yimƙe ta da hatimi, don kada ya ƙara yaudarar al'ummai, har dai shekarun nan dubu su ƙare. Bayan wannan lalle ne a sake shi zuwa ɗan lokaci kaɗan.

4. Sa'an nan na ga kursiyai, da waɗanda aka bai wa ikon hukunci, zaune a kai. Har wa yau, kuma na ga rayukan waɗanda aka fille wa kai saboda shaidar da suka yi wa Yesu, da kuma Maganar Allah, ba su kuwa yi wa dabbar nan da siffarta sujada ba, ba su kuma yarda a yi musu alamarta a goshinsu ko a hannunsu ba, sun sāke rayuwa, sun yi mulki tare da Almasihu har shekara dubu.

5. Sauran matattu kuwa, ba su sāke rayuwa ba, sai bayan da shekaran nan dubu suka cika. Wannan fa shi ne tashin matattu na farko.

Karanta cikakken babi W. Yah 20