Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. Yah 16:13-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Na kuma ga baƙaƙen aljannu masu kama da kwaɗi gudu uku, suna fitowa daga bakin macijin nan, da bakin dabbar nan, da kuma bakin annabin nan na ƙarya,

14. su iskoki ne, aljannu masu yin abubuwan al'ajabi, masu zuwa wurin sarakunan duniya duka, don su tara su saboda yaƙi a babbar ranar nan ta Allah Maɗaukaki.

15. (“Ga ni nan a tafe kamar ɓarawo! Albarka tā tabbata ga wanda yake a zaune a faɗake, yana saye da tufafinsa, don kada ya tafi tsirara, a ga tsiraicinsa.”)

16. Sai suka tattara su a wurin da ake kira Armageddon da Yahudanci.

17. Mala'ika na bakwai ya juye abin da yake a tasarsa a sararin sama, sai aka ji wata murya mai ƙara daga Haikali, wato, daga kursiyin, ta ce, “An gama!”

18. Sai aka yi ta walƙiya, da ƙararraki masu tsanani, da aradu, da wata babbar rawar ƙasa irin wadda ba a taɓa yi ba, tun da ɗan adam yake a duniya, gawurtacciyar rawar ƙasa ƙwarai da gaske.

19. Babban birnin nan kuwa ya rabu gida uku, biranen al'ummai kuma suka fāɗi. Sai Allah ya tuna da Babila mai girma, don ya sa ta, ta sha fushinsa mai tsananin gaske.

20. Kowane tsibiri ya ɓace, manyan duwatsu ma ba a ƙara ganinsu ba.

Karanta cikakken babi W. Yah 16