Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 3:6-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. wanda ya zubo mana a yalwace ta wurin Yesu Almasihu Mai Cetonmu.

7. Wannan kuwa domin a kuɓutar da mu bisa ga alherinsa ne, mu kuma zama magāda masu bege ga rai madawwami.

8. Maganar nan tabbatacciya ce.Ina so ka ƙarfafa waɗannan abubuwa ƙwarai, don waɗanda suka ba da gaskiya ga Allah su himmantu ga aiki nagari, waɗannan abubuwa kuwa masu kyau ne, masu amfani kuma ga mutane.

9. Amma ka yi nesa da gardandamin banza, da ƙididdigar asali, da husuma, da jayayya a kan Shari'a, domin ba su da wata riba, aikin banza ne kuma.

10. Mutumin da yake sa tsattsaguwa kuwa, in ya ƙi kula da gargaɗinka na farko da na biyu, to, sai ka fita sha'aninsa.

11. Ka dai sani irinsa ɓatacce ne, mai yin zunubi, shi kansa ma ya sani haka yake.

12. Sa'ad da na aiko Artimas ko Tikikus zuwa wurinka, sai ka yi matuƙar, ƙoƙari ka zo wurina a Nikafolis, don na yi niyyar cin damuna a can.

13. Ka yi himmar taimakon Zinas, masanin shari'a, da Afolos, su kamo hanya, ka kuma tabbata ba abin da ya gaza musu.

14. Jama'armu su koyi himmantuwa ga aikin kirki don biyan bukatun matsattsu, kada su zama marasa amfani.

15. Duk waɗanda suke tare da ni suna gaishe ka. Ka gayar mini da masoyanmu, masu bangaskiya.Alheri yă tabbata a gare ku, ku duka.

Karanta cikakken babi Tit 3