Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 2:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da 'ya'yansu,

5. su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.

6. Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai.

7. Kai ma sai ka zama gurbi na aiki nagari ta kowace hanya, da koyarwarka kana nuna rashin jirkituwa, da natsuwa,

8. da kuma sahihiyar maganar da ba za a kushe mata ba, don a kunyata abokan hamayya, su rasa hanyar zarginmu.

9. Bayi su yi biyayya ga iyayengijinsu, su kuma gamsar da su ta kowane hali. Kada su yi tsayayya,

10. ko taɓe-taɓe, sai dai su riƙi amana sosai, don su ƙawatar da koyarwar Allah Mai Cetonmu ta kowane hali.

11. Alherin Allah ya bayyana saboda ceton dukkan mutane,

12. yana koya mana mu ƙi rashin bin Allah da mugayen sha'awace-sha'awacen duniya, mu kuma yi zamanmu a duniyar nan da natsuwa, da adalci, da kuma bin Allah,

Karanta cikakken babi Tit 2