Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Tit 2:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Amma kai kam, sai ka faɗi abin da ya dace da sahihiyar koyarwa.

2. Dattawa su kasance masu kamunkai, natsattsu, mahankalta, masu sahihiyar bangaskiya, da ƙauna, da kuma jimiri.

3. Haka kuma, manyan mata su kasance masu keɓaɓɓen hali, ba masu yanke, ko masu jarabar giya ba, su zamana masu koyar da kyakkyawan abu,

4. ta haka su koya wa mata masu ƙuruciya su so mazansu da 'ya'yansu,

5. su kuma kasance natsattsu, masu tsarkin rai, masu kula da gida, masu alheri, masu biyayya ga mazansu, don kada a kushe Maganar Allah.

6. Haka kuma, ka gargaɗi samari su yi kamunkai.

Karanta cikakken babi Tit 2