Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 9:27-33 Littafi Mai Tsarki (HAU)

27. A game da Isra'ila Ishaya ma ya ɗaga murya ya ce, “Ko da yake yawan Isra'ilawa ya kai kamar yashin teku, duk da haka kaɗan ne za su sami ceto.

28. Domin Ubangiji zai zartar da hukuncinsa a duniya, ya gama shi tashi ɗaya.”

29. Kamar yadda Ishaya ya yi faɗa cewa,“Da ba domin Ubangijin Runduna ya bar mana zuriya ba,Da mun zama kamar Saduma,An kuma maishe mu kamar Gwamrata.”

30. To, me kuma za mu ce? Ga shi, al'ummai da ba su nace da neman adalcin Allah ba, sun samu, wato, sun sami adalcin da yake daga bangaskiya.

31. Isra'ila kuwa da suka nace da neman hanyar adalcin Allah, suka kasa samunta.

32. Me ya sa? Don ba su neme ta ta hanyar bangaskiya ba, sai dai ta hanyar aikata aikin lada. Sai suka yi tuntuɓe da dutsen tuntuɓe,

33. kamar yadda yake a rubuce cewa,“Ga shi, na sa dutsen sa tuntuɓe a Sihiyona,Da fā na sa faɗuwa.Duk mai gaskatawa da shi, ba zai kunyata ba.”

Karanta cikakken babi Rom 9