Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 8:16-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Ruhu da Kansa ma, tare da namu ruhu suna yin shaida, cewa mu 'ya'yan Allah ne.

17. In kuwa 'ya'ya muke, ashe, magāda ne kuma, magādan Allah, abokan gādo kuma da Almasihu, in dai har muna shan wuya tare da shi, a kuwa ɗaukaka mu tare da shi.

18. Ai, a ganina, wuyar da muke sha a wannan zamani, ba ta isa a kwatanta ta da ɗaukakar da za a bayyana mana ba.

19. Ga shi, duk halitta tana marmari, tana ɗokin ganin bayyanar 'ya'yan Allah.

20. An sarayar da halitta ta zama banza, ba da nufinta ba, amma da nufin wanda ya sarayar da ita. Duk da haka, akwai sa zuciya,

21. gama za a 'yantar da halitta da kanta ma, daga bautar ruɓewa, domin ta sami 'yancin nan, na ɗaukaka na 'ya'yan Allah.

22. Mun dai san dukan halitta tana nishi, na shan azaba kuma irin ta mai naƙuda, har ya zuwa yanzu.

23. Banda haka ma, har mu kanmu da muka riga muka sami Ruhu Mai Tsarki, wanda yake shi ne nunan fari, a cikin abubuwan da za mu samu, muna nishi a ranmu, muna ɗokin cikar zamanmu na 'ya'yan Allah, wato, fansar jikin nan namu ke nan.

24. Sa'ad da aka cece mu ne muka yi wannan sa zuciya. Amma kuwa, ai, sa zuciya ga abin da aka samu, ba sa zuciya ba ce. Wa yake sa zuciya ga abin da ya samu?

25. In kuwa muna sa zuciya ga abin da ba mu samu ba, da jimiri mukan yi sauraronsa.

Karanta cikakken babi Rom 8