Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 8:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Saboda haka a yanzu, ba sauran kayarwa ga waɗanda suke na Almasihu Yesu.

2. Ka'idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta 'yanta ni daga ka'idar zunubi da ta mutuwa.

3. Abin da ba shi yiwuwa Shari'a ta yi domin ta kasa saboda halin ɗan adam, Allah ya yi shi, wato ya ka da zunubi a cikin jiki, da ya aiko da Ɗansa da kamannin jikin nan namu mai zunubi, domin kawar da zunubi.

4. Wannan kuwa domin a cika hakkokin Shari'a ne a gare mu, mu da ba zaman halin mutuntaka muke yi ba, sai dai na Ruhu.

5. Masu zaman halin mutuntaka, ai, ƙwallafa ransu ga al'amuran halin mutuntaka suke yi, masu zaman Ruhu kuwa ga al'amuran Ruhu.

6. Ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka ƙarshensa mutuwa ne, ƙwallafa rai ga ala'muran Ruhu kuwa rai ne da salama.

7. Don ƙwallafa rai ga al'amuran halin mutuntaka gāba ne da Allah, gama ba ya bin Shari'ar Allah, ba kuwa zai iya ba.

8. Masu zaman halin mutuntaka, ba dama su faranta wa Allah rai.

9. Amma ku kam, ba masu zaman halin mutuntaka ba ne, masu zaman Ruhu ne, in dai har Ruhun Allah yana zaune a zuciyarku. Duk wanda ba shi da Ruhun Almasihu kuwa, ba na Almasihu ba ne.

10. In kuwa Almasihu yana a zuciyarku, ba ruwan jikinku da zunubi ke nan, Ruhu kuwa rai ne a gare ku saboda kun sami adalcin Allah.

11. In kuwa Ruhun wannan da ya ta da Yesu daga matattu yana zaune a zuciyarku, to, shi da ya ta da Almasihu Yesu daga matattu zai kuma raya jikin nan naku mai mutuwa, ta wurin Ruhunsa da yake a zaune a zuciyarku.

12. Domin haka, 'yan'uwa, kun ga halin mutuntaka ba shi da wani hakki a kanmu har da za mu yi zamansa.

Karanta cikakken babi Rom 8