Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 6:17-23 Littafi Mai Tsarki (HAU)

17. Amma godiya tā tabbata ga Allah, ko da yake dā can ku bayin zunubi ne, a yanzu kam kuna biyayya da zuciya ɗaya ga irin koyarwar nan da aka yi muku.

18. Da aka 'yanta ku kuma daga bautar zunubi, kun zama bayin aikin adalci.

19. Mai da magana nake yi irin ta yau da kullum, saboda rarraunar ɗabi'arku. Wato, kamar yadda dā can kuka miƙa gaɓoɓinku ga bautar rashin tsarki, da mugun aiki a kan mugun aiki, haka kuma a yanzu sai ku miƙa gaɓoɓinku ga bautar aikin adalci, domin aikata tsarkakan ayyuka.

20. Sa'ad da kuke bayin zunubi, ba ruwanku da aikin adalci.

21. To, wace fa'ida kuka samu a lokacin nan, a game da aikin da kuke jin kunya a yanzu? Lalle ƙarshen irin wannan aiki mutuwa ne.

22. Amma a yanzu da aka 'yanta ku daga bautar zunubi, kun zama bayin Allah, sakamakonku shi ne tsarkakewa, ƙarshenta kuwa rai madawwami ne.

23. Gama sakamakon zunubi mutuwa ne, amma baiwar Allah ita ce rai madawwami a cikin Almasihu Yesu Ubangijinmu.

Karanta cikakken babi Rom 6