Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 5:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. To, da yake mu kuɓutattu ne ta wurin bangaskiya, muna da salama ke nan a gun Allah, ta wurin Ubangijinmu Yesu Almasihu.

2. Ta wurinsa kuma muka sami shiga alherin nan da muke a ciki, saboda bangaskiyarmu, muna kuma taƙama da sa zuciyarmu ga samun ɗaukakar nan ta Allah.

3. Banda haka ma, har muna taƙama da shan wuyarmu, da yake mun sani shan wuya take sa jimiri,

4. jimiri kuma yake sa ingataccen hali, ingataccen hali kuma yake sa sa zuciya,

5. ita sa zuciyar nan kuwa ba ta sāce iska faufau, domin Allah ya kwarara ƙaunarsa a zukatanmu, ta wurin Ruhu Mai Tsarki da aka ba mu.

6. Tun muna raunana tukuna, Almasihu ya mutu a daidaitaccen lokaci, domin marasa bin Allah.

7. Da ƙyar za a sami wanda zai ba da ransa, saboda mutum mai adalci, ko da yake watakila saboda mutum mai nagarta wani ma sai yă yi kasai da ransa.

8. Amma kuwa Allah yana tabbatar mana da ƙaunar da yake yi mana, wato tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu dominmu.

Karanta cikakken babi Rom 5