Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 13:6-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Shi ne ma ya sa kuke biyan haraji, don su mahukunta ma'aikata ne na Allah, suna kuma yin wannan aiki a koyaushe.

7. Ku ba kowa hakkinsa, masu haraji, harajinsu, masu kuɗin fito, kuɗinsu na fito, waɗanda suka cancanci ladabi, ladabi, waɗanda suka cancanci girmamawa, girmamawa.

8. Kada hakkin kowa ya zauna a kanku, sai dai na ƙaunar juna, don mai ƙaunar maƙwabcinsa ya cika Shari'a ke nan.

9. Umarnan nan cewa, “kada ka yi zina, kada ka yi kisankai, kada ka yi sata, kada ka yi ƙyashi,” da dai duk sauran umarnai an ƙunshe su ne a wannan kalma cewa, “Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.”

10. Ƙauna ba ta cutar maƙwabci saboda haka ƙauna cika Shari'a ce.

11. Ga shi kuma, kun dai san irin zamanin da muke a ciki, ai, lokaci ya riga ya yi da za ku farka daga barci. Gama yanzu mun fi kusa da ceton nan namu a kan sa'ad da muka fara ba da gaskiya.

12. Dare fa ya ƙure, gari ya kusa wayewa. Sai mu watsar da ayyukan duhu, mu yi ɗamara da kayan ɗamara na haske.

13. Mu tafiyar da al'amuranmu yadda ya dace a yi da rana, ba a cikin shashanci da buguwa, ko fasikanci da fajirci, ko jayayya da kishi ba.

14. Amma ku ɗauki halin Ubangiji Yesu Almasihu, kada kuwa ku tanadi halin mutuntaka, don biye wa muguwar sha'awarsa.

Karanta cikakken babi Rom 13