Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 11:18-34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. kada ka yi wa sauran rassan alwashi. In kuwa ka yi, ka tuna fa, ba kai kake ɗauke da saiwar ba, saiwar ce take ɗauke da kai.

19. Kila za ka ce, “Ai, an sare rassan nan ne, don a ɗaura aure da ni.”

20. Hakika haka ne, amma saboda rashin bangaskiyarsu ne aka sare su, kai kuwa saboda bangaskiyarka ne kake kafe. Kada fa ka nuna alfarma, sai dai ka ji tsoron Allah.

21. Da yake Allah bai bar rassan asalin ba, kai ma ba zai bar ka ba.

22. Dubi fa alherin Allah da kuma tsananinsa, wato, tsanani ga waɗanda suka fāɗi, alherinsa kuwa a gare ka, muddin ka ɗore a cikin alherin. In ba haka ba, kai ma sai a datse ka.

23. Ko su ma, in dai ba su nace wa rashin bangaskiyarsu ba, sai a ɗaura aure da su, domin Allah yana da ikon sāke mai da su.

24. Kai ma da aka saro daga zaitun ɗin da asalinsa yake na jeji, aka ɗaura aure da kai a jikin zaitun ɗin na gida, saɓanin yadda aka saba, balle waɗannan rassa na asali, da za a ɗaura aure da su a jikin zaitun ɗin nan nasu na asali?

25. 'Yan'uwa, ga wata asirtacciyar gaskiya da nake so ku sani, domin kada ku zaci ku masu hikima ne, taurarewar nan–wadda ba mai tabbata ba ce–ta sami Isra'ilawa ne, har adadin al'ummai masu ɗungumawa zuwa ga Allah ya cika.

26. Ta haka nan ne Isra'ila duka za su sami ceto, kamar yadda yake a rubuce cewa,“Mai Ceto zai zo daga Sihiyona,Zai kuma kawar da rashin bin Allah daga zuriyar Yakubu,”

27. “Cikar alkawarina a gare su ke nan,Sa'ad da na ɗauke musu zunubansu.”

28. A game da bishara kuma, maƙiyan Allah ne su, domin amfaninku ne kuwa. Amma a game da zaɓen Allah, su ƙaunatattunsa ne, albarkacin kakannin kakanninsu.

29. Domin baiwar Allah da kiransa ba sa tashi.

30. Kamar yadda kuka ƙi bin Allah a dā, amma a yanzu aka yi muku jinƙai saboda rashin biyayyarsu,

31. haka su ma da suke marasa biyayya a yanzu, yanzu a yi musu jinƙai kamar yadda aka yi muku.

32. Don Allah ya kulle kowa a cikin rashin biyayya, domin ya nuna jinƙai ga kowa.

33. Zurfin hikimar Allah da na saninsa da rashin iyaka suke! Hukunce-hukuncensa sun fi gaban bincikewa, hanyoyinsa kuma sun fi gaban bin diddigi!

34. “Wa ya taɓa sanin zuciyar Ubangiji?Ko kuwa wa ya taɓa ba shi wata shawara?”

Karanta cikakken babi Rom 11