Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 10:15-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. Ta ƙaƙa kuma za su yi wa'azi, in ba aikarsu aka yi ba? Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Yaya zai kasance a isowar masu kawo bishara!”

16. Amma ba duka ne suka yi na'am da bisharar ba. Ishaya ma ya ce, “Ya Ubangiji, wa ya gaskata jawabinmu?”

17. Ashe, bangaskiya ta wurin jawabin da ake ji take samuwa, jawabin da ake ji kuma ta Maganar Almasihu yake.

18. Amma ina tambaya. Ba su ji jawabin ba ne? Hakika sun ji.“Muryarsu ta gama duniya duka,Maganarsu kuma ta kai har bangon duniya.”

19. Har wa yau, ina tambaya. Shin, Isra'ila kam, ba su fahimta ba ne? Da farko dai Musa ya ce,“Zan sa ku kishin waɗanda ba al'umma ba ne,Zan kuma sa ku fushi da wata al'ummar marar fahimta.”

20. Ishayan kuma ya fito gabagaɗi ƙwarai ya ce,“Waɗanda ba su neme ni ba, su suka same ni.Na bayyana kuma ga waɗanda ba su taɓa neman sanina ba.”

21. Amma a game da isra'ila, sai ya ce, “Yini zubur ina miƙa hannuwana ga jama'a marasa biyayya, masu tsayayya.”

Karanta cikakken babi Rom 10