Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 10:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ya 'yan'uwa, muradin zuciyata da kuma roƙona ga Allah saboda su, shi ne su sami ceto.

2. Na dai shaida su a kan suna da himmar bauta wa Allah, amma ba da cikakken sani ba.

3. Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar.

4. Domin Almasihu shi ne cikamakin Shari'a, domin kowane mai ba da gaskiya yă sami adalcin Allah.

5. Gama Musa ya rubuta zancen adalcin da yake samuwa ta wurin bin Shari'a, cewa mai iya aikata ta zai rayu ta wurinta.

6. Amma, a game da samun adalcin Allah wanda yake ta wurin bangaskiya ya ce, Kada ka ce a ranka, “Wa zai hau zuwa sama?” Wato, yă sauko da Almasihu.

7. Ko kuwa, “Wa zai gangara can ƙasa?” Wato yă ta da Almasihu daga matattu.

8. Amma me Nassi ya ce? “Maganar, ai, tana kusa da kai, tana ma a bakinka, da kuma a cikin zuciyarka.” Ita ce maganar bangaskiya da muke wa'azi.

9. Wato, in kai da bakinka ka bayyana yarda, cewa Yesu Ubangiji ne, ka kuma gaskata a zuciyarka Allah ya tashe shi daga matattu, za ka sami ceto.

10. Domin da zuci mutum yake gaskatawa yă sami adalcin Allah, da baki yake shaidawa yă sami ceto.

11. Gama Nassi ya ce, “Duk mai gaskatawa da shi ba zai kunyata ba.”

12. Ai, ba wani bambanci a tsakanin Bayahude da Ba'al'umme. Ubangijin nan ɗaya shi ne Ubangijin kowa, mayalwacin baiwa ne kuma ga dukkan masu addu'a a gare shi.

13. “Duk wanda kuwa ya yi addu'a da sunan Ubangiji zai sami ceto.”

14. Amma ta ƙaƙa za su yi addu'a ga wanda ba su gaskata da shi ba? Ta ƙaƙa kuma za su gaskata da wanda ba su taɓa ji ba? Ta ƙaƙa kuma za su ji, in ba mai wa'azi?

Karanta cikakken babi Rom 10