Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 1:16-30 Littafi Mai Tsarki (HAU)

16. Gama ba na jin kunyar bishara, domin ita ce ikon Allah mai kai kowane mai ba da gaskiya ga samun ceto, Yahudawa da fari, sa'an nan kuma al'ummai.

17. Gama bishara ɗin ta bayyana wata hanyar samun adalci a gaban Allah, hanyar nan kuwa ta bangaskiya ce, tun daga farko har zuwa ƙarshe, yadda yake a rubuce cewa, “Wanda yake da adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.”

18. Gama ana bayyana fushin Allah daga Sama, a kan dukan rashin bin Allah, da aikin mugunta na mutanen da suke danne gaskiya, ta aikin muguntarsu,

19. Domin abin da za a iya sani a game da Allah a bayyane yake a gare su, gama Allah ne ya bayyana musu shi.

20. Gama tun daga halittar duniya al'amuran Allah marasa gănuwa, wato ikonsa madawwami, da allahntakarsa, sun fahimtu sarai, ta hanyar abubuwan da aka halitta kuma ake gane su. Saboda haka mutane sun rasa hanzari.

21. Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.

22. Suna da'awa cewa, su masu hikima ne, sai suka zama wawaye.

23. Sun sauya ɗaukakar Allah marar mutuwa da misalin siffar mutum mai mutuwa, da ta tsuntsaye, da ta dabbobi, da kuma ta masu jan ciki.

24. Saboda haka Allah ya sallama su ga rashin tsarkaka ta mugayen sha'awace-sha'awacensu, har su wulakanta jikinsu a junansu,

25. saboda sun sauya gaskiyar Allah da ƙarya, har yi wa halitta ibada, sun kuma bauta mata, sun ƙi su yi wa Mahalicci, shi wanda yabo ya tabbata a gare shi har abada. Amin.

26. Don haka Allah ya sallama su ga mugayen sha'awace-sha'awace masu banƙyama, har matansu suka sauya ɗabi'arsu ta halal, da wadda take ta haram.

27. Haka kuma maza suka bar ma'amalarsu ta halal da mata, jarabar juna ta ɗebe su, maza da maza suna aikata rashin kunya, suna jawo wa kansu sakamako daidai da bauɗewarsu.

28. Tun da yake sun ƙi su yarda su san Allah, Allah ya sallama su ga halin banza, su aikata abin kunya.

29. Su masu aikata rashin adalci ne ƙwarai, da mugunta, da kwaɗayi, da ƙeta. Masu hassada ne, da kisankai, da jayayya, da ha'inci, da kuma nukura gaya matuƙa. Macizan ƙaiƙayi ne,

30. da masu yanke, da maƙiyan Allah, da masu cin mutunci, da masu girmankai, da masu ruba, da masu haddasa mugunta, da marasa bin iyaye,

Karanta cikakken babi Rom 1