Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rom 1:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Daga Bulus, bawan Yesu Almasihu, manzo kirayayye, keɓaɓɓe domin yin bisharar Allah,

2. wadda Allah ya yi alkawari tun dā, ta bakin annabawansa a cikin Littattafai masu tsarki.

3. Bishara ɗin nan a kan Ɗansa ce, Ubangijinmu Yesu Almasihu, wanda ga jiki shi zuriyar Dawuda ne,

4. amma ga tsarkinsa na ruhu shi Ɗan Allah ne, da iko aka ayyana shi haka ta wurin tashinsa daga matattu.

5. Ta wurinsa ne muka sami alheri da kuma manzanci, saboda sunansa dukan al'ummai su gaskata su yi biyayya,

6. a cikinsu kuma har da ku da kuke kirayayyun Yesu Almasihu.

7. Daga Bulus zuwa ga dukan ƙaunatattun Allah da kuke a Roma, tsarkaka kirayayyu.Alheri da salama na Allah Ubanmu, da na Ubangiji Yesu Almasihu su tabbata a gare ku.

8. Da farko dai ina gode wa Allahna ta wurin Yesu Almasihu saboda ku duka, domin ana baza labarin bangaskiyarku a ko'ina a duniya.

9. Domin kuwa Allah, wanda nake bauta wa a ruhuna ta yin bisharar Ɗansa, shi ne mashaidina a kan yadda kullum ba na fasa ambatonku a cikin addu'ata,

Karanta cikakken babi Rom 1