Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 9:6-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Amma domin ku sakankance Ɗan Mutum yana da ikon gafarta zunubi a duniya”–sai ya ce wa shanyayyen–“Tashi, ka ɗauki shimfiɗarka ka tafi gida.”

7. Shi kuwa ya tashi ya tafi gida.

8. Da taron suka ga haka, sai tsoro ya kama su, suka ɗaukaka Allah, wanda ya ba mutane iko haka.

9. Da Yesu ya yi gaba, ya ga wani mutum mai suna Matiyu a zaune, yana aiki a wurin karɓar haraji. Ya ce masa, “Bi ni.” Sai ya tashi ya bi shi.

10. Sa'ad da kuwa Yesu yake cin abinci a gida, sai ga masu karɓar haraji da masu zunubi da yawa sun zo, sun zauna tare da shi da almajiransa.

11. Da Farisiyawa suka ga haka, sai suka ce wa almajiransa, “Don me malaminku yake ci tare da masu karɓar haraji da masu zunubi?”

12. Amma da Yesu ya ji haka ya ce, “Ai, lafiyayyu ba ruwansu da likita, sai dai marasa lafiya.

Karanta cikakken babi Mat 9