Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 7:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Kada ku ɗora wa kowa laifi, don kada a ɗora muku.

2. Don da irin hukuncin da kuka zartar, da shi za a zartar muku. Mudun da kuka auna, da shi za a auna muku.

3. Don me kake duban ɗan hakin da yake idon ɗan'uwanka, amma gungumen da yake a naka ido ba ka kula ba?

4. Ko kuwa yaya za ka iya ce wa ɗan'wanka, ‘Bari in cire maka ɗan hakin daga idonka,’ alhali kuwa da gungume a naka ido?

5. Kai munafuki! Sai ka fara cire gungumen da yake idonka tukuna, sa'an nan ka gani sosai yadda za ka cire ɗan hakin daga idon ɗan'uwanka.

6. “Kada ku ba karnuka abin da yake tsattsarka. Kada kuma ku jefa wa alhanzir lu'ulu'unku, don kada su tattake su, su juyo su kyakketa ku.”

7. “Ku yi ta roƙo, za a ba ku. Ku yi ta nema, za ku samu. Ku yi ta ƙwanƙwasawa, za a kuwa buɗe muku.

8. Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu. Wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.

9. To, wane ne a cikinku, ɗansa zai roƙe shi gurasa, ya ba shi dutse?

10. Ko kuwa ya roƙe shi kifi, ya ba shi maciji?

11. To, ku da kuke mugaye ma, kuka san yadda za ku ba 'ya'yanku kyautar kyawawan abubuwa, balle Ubanku na Sama da zai ba da abubuwan alheri ga masu roƙonsa?

12. Saboda haka duk abin da kuke so mutane su yi muku, ku ma sai ku yi musu, domin wannan shi ne Attaura da koyarwar annabawa.”

13. “Ku shiga ta ƙunƙuntar ƙofa, gama ƙofa zuwa hallaka faffaɗa ce, hanyarta mai sauƙin bi ce, masu shiga ta cikinta suna da yawa.

14. Domin kuwa ƙofar zuwa rai ƙunƙunta ce, hanyarta mai wuyar bi ce, masu samunta kuwa kaɗan ne.”

Karanta cikakken babi Mat 7