Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 6:8-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

8. Kada ku zama kamarsu, domin Ubanku ya san bukatarku tun kafin ku roƙe shi.

9. Saboda haka sai ku yi addu'a kamar haka,‘Ya Ubanmu, wanda yake cikin Sama,A kiyaye sunanka da tsarki.

10. Mulkinka yă zo,A aikata nufinka a duniya kamar yadda ake yi a Sama.

11. Ka ba mu abincinmu na yau.

12. Ka gafarta mana laifofinmu,Kamar yadda mu ma muke gafarta wa waɗanda suke yi mana laifi.

13. Kada ka kai mu wurin jaraba,Amma ka cece mu daga Mugun.’

14. Domin in kun yafe wa mutane laifofinsu, Ubanku na Sama zai yafe muku.

15. In kuwa ba ku yafe wa mutane laifofinsu ba, Ubanku ma ba zai yafe muku naku ba.”

16. “In kuma kuna yin azumi, kada ku turɓune fuska kamar munafukai, don sukan yanƙwane fuska, wai don mutane su ga suna azumi ne. Hakika, ina gaya muku, sun sami iyakar ladansu ke nan.

17. Amma in kana azumi, ka shafa mai a ka, ka kuma wanke fuska,

18. don kada mutane su ga alama kana azumi, sai dai Ubanku da yake ɓoye ya gani. Ubanku kuma da yake ganin abin da ake yi a asirce, zai sāka maka.”

19. “Kada ku tara wa kanku dukiya a duniya, inda asu da tsatsa suke ɓatawa, inda ɓarayi kuma suke karyawa su yi sata.

20. Sai dai ku tara wa kanku dukiya a Sama, inda ba asu da tsatsa da za su ɓata, inda kuma ba ɓarayin da za su karya su yi sata.

21. Domin kuwa inda dukiyarka take, a nan zuciyarka ma take.”

Karanta cikakken babi Mat 6