Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 28:4-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Saboda tsoronsa sai masu tsaro suka ɗau makyarkyata, har suka yi kamar sun mutu.

5. Amma sai mala'ikan ya ce wa matan, “Kada ku ji tsoro, domin na sani Yesu kuke nema, wanda aka gicciye.

6. Ai, ba ya nan. Ya tashi, yadda ya faɗa. Ku zo ku ga wurin da aka sa shi.

7. Ku tafi maza ku gaya wa almajiransa, cewa, ya tashi daga matattu. Ga shi kuma, zai riga ku zuwa ƙasar Galili, a can ne za ku gan shi. Ga shi, na gaya muku.”

8. Sai suka tashi daga kabarin da gaggawa da tsoro, game da matuƙar farin ciki, suka ruga a guje su kai wa almajiransa labari.

9. Sai kuwa ga Yesu ya tarye su, ya ce, “Salama alaikun!” Suka matso suka rungume ƙafafunsa, suka yi masa sujada.

10. Sai Yesu ya ce musu, “Kada ku ji tsoro, ku je ku gaya wa 'yan'uwana su tafi ƙasar Galili, a can ne za su gan ni.”

11. Suna tafiya ke nan, sai waɗansu daga cikin sojan nan suka shiga birni, suka ba manyan firistoci labarin da ya auku.

12. Su kuwa da suka taru da shugabannin jama'a suka yi shawara, sai suka ba sojan kuɗi masu tsoka,

Karanta cikakken babi Mat 28