Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:32-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Suna tafiya ke nan, sai suka gamu da wani Bakurane, mai suna Saminu. Shi ne suka tilasta wa ya ɗauki gicciyen Yesu.

33. Da suka isa wurin da ake kira Golgota, wato, wurin ƙoƙwan kai,

34. suka miƙa masa ruwan inabi gauraye da wani abu mai ɗaci yă sha, amma da ya ɗanɗana sai ya ƙi sha.

35. Da suka gicciye shi, suka rarraba tufafinsa a junansu ta jefa kuri'a.

36. Suka zauna a nan suna tsaronsa.

37. A daidai kansa aka kafa sanarwar laifinsa cewa, “Wannan shi ne Yesu, Sarkin Yahudawa.”

38. Sai kuma aka gicciye 'yan fashi biyu tare da shi, ɗaya a dama, ɗaya a hagun.

39. Masu wucewa suka yi ta yi masa baƙar magana, suna kaɗa kai,

40. suna cewa, “Kai da za ka rushe Haikalin, ka kuma gina shi a cikin kwana uku, ceci kanka mana! In kai Ɗan Allah ne, to sauko daga gicciyen mana!”

Karanta cikakken babi Mat 27