Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 27:18-31 Littafi Mai Tsarki (HAU)

18. Don ya sani saboda hassada ne suka bashe shi.

19. Banda haka kuma, a lokacin da yake zaune a kan gadon shari'a, sai mata tasa ta aiko masa da cewa, “Ka fita daga sha'anin mara laifin nan, don yau na sha wahala ƙwarai a mafarkinsa.”

20. To, sai manyan firistoci da shugabanni suka rarrashi jama'a su zaɓi Barabbas, Yesu kuwa a kashe shi.

21. Sai mai mulki ya sāke ce musu, “Wane ne a cikin biyun nan kuke so in sakar muku?” Sai suka ce, “Barabbas.”

22. Bilatus ya ce musu, “To, ƙaƙa zan yi da Yesu da ake kira Almasihu?” Duk sai suka ce, “A gicciye shi!”

23. Ya ce, “Ta wane halin? Wane mugun abu ya yi?” Amma su sai ƙara ɗaga murya suke ta yi, suna cewa, “A gicciye shi!”

24. Da Bilatus ya ga bai rinjaye su ba, sai dai hargitsi yana shirin tashi, sai ya ɗibi ruwa ya wanke hannunsa a gaban jama'a, ya ce, “Ni kam, na kuɓuta daga alhakin jinin mai adalcin nan. Wannan ruwanku ne.”

25. Sai duk jama'a suka amsa suka ce, “Alhakin jininsa a wuyanmu, mu da 'ya'yanmu!”

26. Sa'an nan ya sakar musu Barabbas. Bayan ya yi wa Yesu bulala, sai ya ba da shi a gicciye shi.

27. Sai sojan mai mulki suka kai Yesu cikin fadar mai mulki, suka tara dukan ƙungiyar soja a kansa.

28. Sai suka tuɓe shi, suka yafa masa wata jar alkyabba.

29. Suka yi wani rawani na ƙaya, suka sa masa a kā, suka danƙa masa sanda a hannunsa na dama, suka kuma durƙusa a gabansa, suna yi masa ba'a suna cewa, “Ranka ya daɗe, Sarkin Yahudawa!”

30. Suka tattofa masa yau, suka karɓe sandan, suka ƙwala masa a ka.

31. Da suka gama yi masa ba'a, sai suka yaye masa alkyabbar, suka sa masa nasa tufafi, suka tafi da shi su gicciye shi.

Karanta cikakken babi Mat 27