Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:34-45 Littafi Mai Tsarki (HAU)

34. Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

35. Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.

36. Sa'an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu'a.”

37. Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.

38. Sai ya ce musu, “Raina yana shan wahala matuƙa, har ma kamar in mutu. Ku dakata a nan, ku zauna a faɗake tare da ni.”

39. Da ya ci gaba kaɗan, sai ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu'a ya ce, “Ya Ubana, in mai yiwuwa ne, ka ɗauke mini ƙoƙon wahalar nan. Duk da haka dai ba nufina ba, sai naka.”

40. Ya komo wurin almajiran, ya ga suna barci, sai ya ce wa Bitrus, “Ashe, ba za ku iya zama a faɗake tare da ni ko da na sa'a ɗaya ba?

41. Ku zauna a faɗake, ku yi addu'a, kada ku faɗa ga gwaji. Lalle ruhu ya ɗauka, amma jiki rarrauna ne.”

42. Har wa yau a komawa ta biyu, sai ya je ya yi addu'a, ya ce, “Ya Ubana, in wannan ba zai wuce ba sai na sha shi, to, a aikata nufinka.”

43. Har yanzu dai ya dawo ya ga suna barci, don duk barci ya cika musu ido.

44. Har wa yau ya sāke barinsu, ya koma ya yi addu'a ta uku, yana maimaita maganar dā.

45. Sai ya komo wurin almajiran, ya ce musu, “Har yanzu barci kuke yi, kuna hutawa? To, ga shi, lokaci ya yi kusa. An ba da Ɗan Mutum ga masu zunubi.

Karanta cikakken babi Mat 26