Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 26:26-37 Littafi Mai Tsarki (HAU)

26. Suna cikin cin abinci, sai Yesu ya ɗauki gurasa, ya yi godiya ga Allah, ya gutsuttsura, ya ba almajiran, ya ce, “Ungo, ku ci. Wannan jikina ne.”

27. Sai ya ɗauki ƙoƙo bayan ya kuma yi godiya ga Allah, sai ya ba su, ya ce, “Dukkanku ku shassha.

28. Wannan jinina ne na tabbatar alkawari, wanda za a zubar saboda mutane da yawa, domin gafarar zunubansu.

29. Ina gaya muku, ba zan ƙara shan ruwan inabi ba, sai dai a ranar nan da za mu sha wani sabo tare da ku a Mulkin Ubana.”

30. Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.

31. Sai Yesu ya ce musu, “Duk za ku yi tuntuɓe sabili da ni a wannan dare domin a rubuce yake cewa, ‘Zan bugi makiyayi, tumakin garken kuwa za su fasu.’

32. Amma fa bayan an tashe ni, zan riga ku zuwa ƙasar Galili.”

33. Bitrus ya ce masa, “Ko duk sun yi tuntuɓe sabili da kai, ni kam ba zan yi tuntuɓe ba faufau.”

34. Yesu ya ce masa, “Hakika, ina gaya maka, ko a wannan dare, kafin carar zakara, za ka yi musun sanina sau uku.”

35. Bitrus ya ce masa, “Ko za a kashe ni tare da kai, ba zan yi musun saninka ba.” Haka ma duk almajiran suka ce.

36. Sa'an nan Yesu ya zo da su wani wuri da ake kira Gatsemani. Ya ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, Ni kuwa zan je can in yi addu'a.”

37. Sai ya ɗauki Bitrus da 'ya'yan nan na Zabadi biyu, ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.

Karanta cikakken babi Mat 26