Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 25:23-38 Littafi Mai Tsarki (HAU)

23. Sai ubangijinsa ya ce masa, ‘Madalla, bawan kirki, mai aminci. Kā yi gaskiya a kan ƙaramin abu, zan ɗora ka a kan mai yawa. Ka zo ku yi farin ciki tare da ubangijinka.’

24. Shi kuma wanda ya karɓi talanti guda ɗin, sai ya matso, ya ce, ‘Ya ubangiji, na sani kai mutum ne mai tsanani, kana son girbi inda ba kai ka shuka ba, mai son banza ne.

25. Shi ya sa na ji tsoro, har na je na yi tono na ɓoye talantinka. To, ga kayanka nan!’

26. Sai ubangijinsa ya amsa masa ya ce, ‘Kai mugun bawa, malalaci! Ashe, ka sani ina girbi inda ba ni na shuka ba, ni kuma mai son banza ne?

27. Ya kamata ka sa kuɗina a ma'aji, da na dawo kuma da sai in karɓi abina har da riba!

28. Don haka sai ku karɓe talantin daga gunsa, ku bai wa mai goman nan.

29. Don duk mai abu a kan ƙara wa, har ya yalwata. Marar abu kuwa, ko ɗan abin da yake da shi ma, sai an karɓe masa.

30. Ku kuma jefa banzan bawan nan a baƙin duhu. Nan za a yi kuka da cizon baki.’ ”

31. “Sa'ad da Ɗan Mutum ya zo cikin ɗaukakarsa tare da mala'iku duka, sa'an nan ne zai zauna a maɗaukakin kursiyinsa.

32. Za a tara dukan al'ummai a gabansa, zai kuma ware su dabam dabam, kamar yadda makiyayi yake ware tumaki da awaki.

33. Zai sa tumaki a damansa, awaki kuwa a hagunsa.

34. Sa'an nan ne Sarki zai ce wa waɗanda suke dama da shi, ‘Ku zo, ya ku da Ubana ya yi wa albarka, sai ku gāji mulkin da aka tanadar muku tun daga farkon duniya.

35. Domin na ji yunwa, kun ba ni abinci. Na ji ƙishirwa, kun ba ni na sha. Na yi baƙunci, kun saukar da ni.

36. Na yi huntanci, kun tufasar da ni. Na yi rashin lafiya, kun ziyarce ni. Ina kurkuku, kun kula da ni.’

37. Sa'an nan ne masu adalci za su amsa masa su ce, ‘Ya Ubangiji, a yaushe muka gan ka da yunwa muka cishe ka, ko kuwa da ƙishirwa muka shayar da kai?

38. A yaushe kuma muka gan ka baƙo muka sauke ka, ko kuwa huntu muka tufasar da kai?

Karanta cikakken babi Mat 25