Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mat 25:10-18 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Tun suna wajen sayen, sai angon ya iso, waɗanda suke shirye suka shiga wurin biki tare da shi, aka kuma rufe ƙofa.

11. Daga baya sai waɗancan 'yan matan ma suka iso, suka ce, ‘Ya Ubangiji, ya Ubangiji, ka buɗe mana!’

12. Sai ya amsa ya ce, ‘Hakika, ina gaya muku, ni ban san ku ba.’

13. Don haka, sai ku zauna a faɗake, don ba ku san ranar ba, ko kuwa sa'ar.”

14. “Kamar mutum ne da zai yi tafiya, ya kira bayinsa, ya danƙa musu dukiyarsa.

15. Ya ba ɗaya talanti biyar, ɗaya talanti biyu, wani kuma ya ba shi ɗaya, kowa dai gwargwadon ƙarfinsa. Sa'an nan ya tafi.

16. Shi wanda ya karɓi talanti biyar ɗin nan, nan da nan sai ya je ya yi ta jujjuya su, har wuri ya bugi wuri.

17. Haka kuma wanda ya karɓi talanti biyu, shi ma sai wuri ya bugi wuri.

18. Amma wannan da ya karɓi talanti ɗaya ɗin, sai ya je ya tona rami ya ɓoye kuɗin ubangijinsa.

Karanta cikakken babi Mat 25